Shugaba Bola Ahmed Tinubu Ya Bada Buhunan Shinkafa Ga Ministocin Najeriya Don Tallafawa Al’ummar Kasar
Ministan ma’adanai Dokta Alake ya bayyana cewa, “A matsayin martani ga matakin da fadar shugaban kasa ta ɗauka na magance Bukatun ‘yan Najeriya ta hanyar ƙara samar da abinci a matakin kasa, An ware buhunan shinkafa 1,200 ga kowane minista Domin ƙara samar da hanyoyin rarraba kayayyakin da ake da su kamar Gwamnatocin jihohi da kungiyoyin jama’a. ”
Ministan ya kara da cewa, “Za mu tabbatar da cewa wadannan tanade-tanaden an yi su ne ga tsofaffi kawai. A irin waɗannan lokuta, yana da mahimmanci a tallafa wa iyayenmu maza da mata, bisa ga ƙa’idodin Omoluabi na kula da tsofaffi a cikin al’ummominmu.”
Dokta Alake ya kuma bayyana cewa, matakin da za a dauka nan gaba zai shafi sauran kungiyoyi masu rauni, da suka hada da zawarawa, marayu, nakasassu, da Ɗaliban manyan makarantu.