Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya isa Maiduguri don jajantawa al’ummar da iftila’in ambaliya ya Rutsa Dasu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya isa birnin Maiduguri domin jajantawa al’ummar jihar Borno kan iftila’in ambaliyar da ya afkwa wa birnin.
Ziyarar tasa na zuwa ne kwanaki shida bayan mummunar ambaliyar da birnin ya fuskanta wanda rabon a ga haka tun bayan shekara 30 da suka wuce.
Bayan isarsa birnin, kai-tsaye ya garzaya ɗaya daga cikin sansanonin da aka tsugunar da waɗanda lamarin ya ɗaiɗaita domin jajanta musu.
Tinubu ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta tallafawa mutanen.
“Ina son tabbatar muku da cewa za mu tallafa muku domin rage raɗadin da kuka shiga sakamakon wannan iftila’i,” in ji Tinubu.
Tawagar shugaban da ta kai ziyara birnin na Maiduguri ta kunshi shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio da ministan aikin gona Abubakar Kyari da kuma sauran mukarrabai da masu taimaka masa.
Ɓallewar madatsar ruwa ta Alau da ke wajen birnin ce ta haifar da mummunar matsalar.
Ambaliyar ta rutsa da mutum 37 a cewar hukumar ba da agaji ta ƙasa Nema.
Zuwa yanzu gwamnatin jihar ta ce ta yi sanadiyar ɗaiɗaita mutane sama da miliyan ɗaya.