Jami’an hukumar Ƴansanda sun kama ɗaya daga cikin fursinonin da su ka tsere daga gidan yarin Maiduguri
Rundunar ƴansanda a jihar Borno ta sanar da sake kama Abubakar Mohammed, daya daga cikin wadanda aka yankewa hukuncin daurin rai da rai da ya tsere a lokacin rugujewar ginin kantangar gidan gyaran hali ta Maiduguri sakamakon barkewar ambaliyar ruwa a makon da ya gabata.
Daily Trust ta ruwaito yadda katangar gidan ta fadi a lokacin da lamarin ya faru, wanda ya sa wasu fursunoni su ka tsere.
Bayan ta musanta cewa fursunoni sun tsere a lokacin ambaliyar, daga baya hukumomin gidan yarin sun bayyana sunayen fursunoni 274 da su ka tsere.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴansandan jihar Borno, SP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar a yau Talata, ya bayyana cewa an sake kama daya daga cikin wadanda ake zargin.
“Mu na farin cikin sanar da nasarar sake kama wani ɗaurarre da ya tsere, Abubakar Mohammed, mai shekaru 27, wanda ke zaman gidan yari bisa laifin kisan kai kuma ya tsere daga cibiyar tsaro ta Maiduguri.
“A ranar 15 ga Satumba, 2024, da misalin karfe 3 na rana, wani mazaunin unguwar Bulakara, karamar hukumar Gubio, ya sanar da ‘yan sanda bayan ganin Abubakar a garin Gubio biyo bayan tserewar da ya yi daga Cibiyar Kula da Tsaro ta Maiduguri, sakamakon rugujewar katangar da ta yi lokacin ambaliyar ruwa .
“A cikin gaggawa, tawagar ƴansandan da ke sintiri suka garzaya tare da cafke Abubakar da ya tsere, za a mika shi ga hukumar kula da gyaran hali ta Najeriya, kuma ana ci gaba da kokarin zakulo duk wasu da aka samu da laifi a yankin.” in ji shi.