Kimanin Yara huɗu ne suka mutu a cikin firjin
Wasu yara huɗu sun mutu lokacin da suke wasa a cikin wani tsohon firinji a yankin Zambezi da ke arewa maso gabashin ƙasar Namibia, inda tuni Ƴansanda su ka fara gudanar da bincike kan lamarin.
BBC ta rawaito cewa yaran masu shekara uku zuwa shida, an gano su ne a cikin firijin da aka daina amfani da shi a yankin mai cike da cunkoso a garin Katima Mulilo a jiya Litinin da yamma.
Rundunar ‘yan sandan ta yi imanin cewa yaran sun maƙale ne a lokacin da suke wasa, inda suka faɗa ciki, amma ana ci gaba da bincike.
Biyu daga cikin yaran sun mutu nan take a cikin firijin yayin da sauran biyu kuma suka mutu a asibiti lokacin da suke karɓar magani, kamar yadda kafafen yaɗa labarai a yankin suka ruwaito.
“Lokacin da na shigo, na ga jami’an lafiya na kula da ɗiyata da wata yarinya. Sun garzaya da su asibiti, yayin da sauran biyun kuma aka saka su cikin motocin ɗaukar gawawwaki,” in ji Aranges Shoro, mahaifin yaran, akmar yadda ya shaida wa wata jaridar ƙasar ta Namibia.
An sanar da mutuwar sauran yaran biyu bayan garzaya da su asibitin Katima Mulilo da ke kusa, kamar yadda kafar yada labarai ta NBC ta ruwaito.
Daily Nigerian Hausa