Labaran Duniya

Atiku Abubakar Yace Jam’iyar APC ta jefa Najeriya cikin ƙunci da talauci kada ku zaɓe ta a Edo

Atiku Abubakar

Tsohon mataimkain shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya gargaɗi al’ummar jihar Edo da su guji zaɓar ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar da ke tafe ranar Asabar 21 ga watan Satumban, 2024.

Atiku ya bayyana haka ne a shafinsa na X ranar Laraba, inda ya shawarci mazauna jihar da su zaɓi ɗan takara da ya cancanta wanda zai kai jihar gaba.

Ya ce APC ta jefa al’umma cikin mawuyacin hali kuma ba ta jin koke-kokensu.

“A matsayinku na ƴan jihar Edo, ku yi amfani da ƴancinku na yin zaɓe don watsi da rashin shugabanci mai kyau da kuma kawo sauyi. Ku tabbata kun zaɓi cancanta.

“APC ta saba yi wa mutane daɗin baki lokacin yaƙin neman zaɓe, amma da zarar sun yi nasara sai su sauya manufa – jam’iyyar cike take da masu son mulki kawai ba tare da sanya buƙatun al’umma a gaba ba,” in ji Atiku.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriyar ya ce jam’iyyar ta sauka daga tsarin shugabanci nagari tare da yin watsi da buƙatun talakawa.

Ya ce sun jefa ƴan Najeriya cikin wahala da kunshi karkashin jagorancinsu.

Don haka ya buƙaci ƴan jihar ta Edo da su fito su zaɓi ɗan takarar jam’iyyar PDP Dr. Asue Ighodalo wanda a cewarsa shi zai kai jihar gaba.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button