DA ƊUMI-ƊUMI:🔥 Sabon rikici tsakanin ƴan bindiga a Zamfara ya ci rayukan ƙasurguman ƴan bindiga biyu
Daga: Ashiru Lawal Nagoma RuwanƁaure
Wani sabon rikici da ya ɓarke tsakanin dabobin ƴan bindiga a Zamfara ya laƙume rayukan wasu gawurtattun ƴan bindiga biyu da suka yi ƙaurin suna wajen kai miyagun hare-hare a jihar ta Zamfara.
Lamarin dai ya faru ne a yankin Bingi ta ƙaramar hukumar Maru a jihar ta Zamfara, a wani Daji da ke tsakanin Mallawa/Dogon Daji, a daren jiya .
Sahel24 Tv ta ruwaito wani fitaccen ɗan bindiga mai suna Yellow Burwaye, shi ne ya buɗe wa wasu ƙasurguman ƴan bindiga da suka haɗa da Ɗan Nagala da wani Zakiru, wanda shi ne ya kitsa wani mummunan hari a masallaci mutane na tsaka da Sallah tare da kashe wasu da dama da kuma sace wasu ciki har da liman a garin Kanoma a jihar ta Zamfara.
A saƙon da ya wallafa a shafinsa na Fezbuk, wani mazaunin yankin mai suna Mamman Bashar Kanoma, ya ce lamarin ya yi wa al’umma mazauna yankin daɗi nesa ba kusa ba.
Jihar Zamfara dai ita ce kan gaba matuƙa wajen fama da ayyukan ta’addanci, ko da yake a ƴan kwanakin nan an soma ganin hasken lamarin, bayan kisan wani ƙasurgumin ɗan bindigar mai suna Halilu Sububu da sojojin Najeriya suka yi.