EFCC Tace Tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello Bai Zo Hannun Su Ba
Jami’an Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa a Najeriya sun yi watsi da iƙirarin da tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya yi cewa ya amsa gayyatar da suka yi masa a ranar Laraba.
Hukumar ta ce har yanzu tana cigaba da neman tsohon gwamnan bisa zargin halasta kuɗaɗen haram da suka kai naira biliyan 80.2.
Kakakin hukumar, Dele Oyewale, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aike wa manema labarai a Abuja ranar Laraba.
Tun da farko ofishin yaɗa labaran tsohon gwamnan ya faɗa cikin wata sanarwa cewa Bello ya amsa gayyatar da EFCC ta yi masa, inda ya ce ya yanke shawarar yin hakan ne bayan tattaunawa da iyalansa, da ƙungiyar lauyoyi, da kuma abokansa na siyasa.
Sanarwar ta kara da cewa za a bayyana cikakken bayanin yadda al’amura suka gudana tsakanin tsohon gwamnan da jami’an EFCC.
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Ohiare Michael, Daraktan ofishin yaɗa labarai na Yahaya Bello, ta ce: “Muna fatan hukumar za ta nuna ƙwarewa kamar yadda ya kamata tare da mutunta ƴancinsa na ɗan ƙasa a Najeriya.”
Amma da yake mayar da martani kan wannan iƙirari, mai magana da yawun hukumar ta EFCC ya yi mamakin dalilin da zai sa za a aika gayyata ga mutumin da aka ayyana ana neman sa ruwa a jallo kuma a halin yanzu hukumar ke da sammacin kama shi.