Gwamnatin Najeriya ta gargaɗi jihohi 11 kan sako ruwa daga Lagdo dam na Kamaru
Daga Shafin BBC Hausa
Gwamnatin Najeriya ta gargaɗi ƴan ƙasar da su kasance cikin shirin shigowar ruwa daga dam ɗin Labdo na ƙasar Kamaru.
Darakta-Janar na Hukumar Nigeria Hydrological Service Agency (NIHSA), Umar Mohammed, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Sai dai ya buƙaci ƴan Najeriya su kwantar da hankalinsu, inda ya ce ba za a samu mummunar ambaliya ba a Najeriya saboda buɗe dam ɗin.
Sai dai ya ƙara da cewa jihohin Adamawa da Taraba da Kogi da Nasarawa da Benue da Anambra da Bayelsa da Delta da Edo da Kuros Riba da Rivers suna buƙatar fara shirin ko ta kwana domin rage illar ambaliyar idan ta auku.
Dam ɗin Lagdo da yake arewacin Kamaru yana girman 586 km2.
Wata ƙididdiga daga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta nuna cewa da aka sakok ruwan dam ɗin a shekarar 2022, ya jawo mummunar ambaliya, inda mutum 603 suka mutu, sannan sama da mutum miliyan 1.4 suka rasa muhallansu, sannan wasu 2,400 suka jikkata.
Haka ambaliyar ta 2022 ta ɓarnata gidaje 82,035 da hekta 332,327 na gonaki.
A watan Oktoban 2023 ne Majalisar Dattawa ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta waiwayi batun gina madatsar ruwa na Dasin Hausa da sauransu domin su riƙa tare ruwan dam ɗin na Lagdo na Kamaru idan ya malalo, kamar yadda muka kalato daga Daily Trust.