Labaran Duniya

Hukumar @Yansanda Tace Zasu Daina Tsayar Da Motoci Domin Duba Takardu

Ƴansanda
Bayanan hoto,…

Rundunar ƴansanda Najeriya ta sanar da cewa bayan fito da tsarin rajistar bayanan motoci na yanar gizo, babu buƙatar ƴansanda su cigaba da tsayar da motoci suna duba takardu.

Kakarin rundunar, Olumuyiwa Adejobi ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Laraba.

Adejobi ya ƙara da cewa da zarar tsarin rajistar motocin na e-CMR ya fara aiki, masu motoci ba sai sun zo a tantance takardunsu da kansu ba, domin za a tattara bayanan motoci baki ɗaya a yanar gizo.

“Za a daina tsayar da motoci ana duba takardunsu – an horar da jami’anmu amfani da fasahar zamani wajen tantance takardun,” kamar yadda ya bayyana a X.

“Ta hanyar amfani da tsarin na E0CMR, ba sai ka je tantance takardun motarka da kanka ba. Za ka iya yin hakan ta intanet cikin sauri da sauƙi.”

“Idan ka yi rajistar motarka a tsarin NPF E-CMR, sai aka sace ta, dandanan za ka shiga intanet ka nuna motar a matsayin wadda aka sace domin a kama wanda yake ciki.”

Ya ce da zarar ka kunna alamar sace motar a intanet, jami’an ƴansanda a faɗin ƙasar za su ji cikin ƴan daƙiƙa kaɗan, wanda hakan zai sauƙaƙa wajen gano motar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button