Hukumar EFCC ta kama wasu Da Take Zargi Da Laifin Sayen ƙuri’u A Jihar Edo
Jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC, sun kama wasu mutane da suke zargi da sayen ƙuri’a a zaɓen gwamnan jihar Edo da ke gudana a yau Asabar.
An kama mutanen su uku a wata rumfar zaɓe a yankin ƙaramar hukumar Egor da ke jihar.
Jami’an hukumar sun tafi da mutanen maza uku da mace guda.
To sai dai gidan Talbijin na Channels ya ruwaito cewa mutanen gari sun nuna turjiya kan kama mutanen, inda suka yi yunƙurin hana tyafiya da su.
A ranar Juma’a ne dai hukumar ta ce ta tura jami’anta zuwa jihar domin lura da zaɓen.
‘’Sayen ƙuri’a babban laifi ne da ya jiɓanci kuɗi, don haka EFCC ba za ta lamunci wannan ba a ko’ina’’, inji kakakin hukumar Dele Oyewale, kamar yadda gidan Talbijin na Channels ya ambato shi ya faɗi.