JIBWIS ta yi kira ga rundunar sojin Najeriya da ta yi bincike ga lamarin Seaman Abbas kuma ta masa adalci
Daga Shafin Sahel24 TV
Ƙungiyar IZALA tayi ƙira ga rundunar Sojin ƙasa ta Naijeriya (Nigerian Army) da ta gaggauta yin binciken ƙwa-ƙwaf ga lamarin Seaman Abbas Haruna, Sojin ruwan Naijeriya (Nigerian Navy) da ya samu matsala da wani babban sojin ƙasa mai suna burgediya janar MS Adamu wanda ya kulle shi a ma’ajiyar Soji (Gurd Room) dake Abaca Barrack har tsawon shekaru shida, wanda ta kai ga har ya samu taɓin hankali, ya kuma rasa tagwayen ‘ya’yansa.
Shugaban IZALA ta tarayyar Naijeriya Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, shi yayi wannan ƙira a madadin Ƙungiyar, inda yace musulunci addinin zaman lafiya ne, kuma addini ne da yake son adalci da kyautatawa.
Shehin Malamin yace, Babban Sojin Janar MS Adamu ya ɗau matakin tsare Abbas ne domin rahoto ya nuna cewa yaje sallah ne aka nemi hukunta shi, dan haka muke so muji bahasi kan abinda ya faru saboda Addini musulunci Addini ne mai yin Adalci ga kowa da fatan Helkwatar sojoji zasu fitar da cikakken rahoto mai gamsarwa kan lamarin, tabbas muna cike da damuwa saboda tsare shi a Gurd Room har tsawon shekaru shida tabbas wannan lamari ya Sosa zukatan masallata a faɗin Duniya.
A ƙarshe Sheikh Bala ya nemi Shugaban tsaron Naijeriya (Chief of Defence Staff) General Christopher Musa, da Shugaban Sojin Ruwa (CNC) Vice Admiral Emmanuel Ikechukwu Ogalla, da suyi bincike cikin sauri a samawa wannan bawan Allah Seaman Abbas ‘yanci ya koma cikin iyalansa yaci gaba aikinsa matuƙar bincike ya nuna bayi da laifi, kuma ayi gyara domin kaucewa faruwar hakan a gaba.
Tun farko dai anga wani Bidiyon ya nuna yadda matar Abbas Haruna mai suna Hussaina ta zayyana irin halin da mijinta ya shiga bayan da ya samu sabani da shugaban bataliyarsa kan ya je sallah, lamarin da ta ce ya kai ga tsare shi har ma ya haukace.
~JIBWIS NIGERIA
Follow 👉 Sahel24 Tv