Jami’an Tsaro Sun Fitar Da Gwamna Obaseki Daga Ofishin INEC
Jami’an ‘yansanda sun fitar da gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki daga cikin ofishin hukumar zaɓen ƙasar, inda ake tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar.
Rahotoni sun ce cikin dare ne Mista Obaseki ya bayyana a cibiyar tattara sakamakon zaɓen da ke harabar hukumar tare da wasu jami’ai.
To sai dai babban mataimakin sifeton ‘yansandan ƙasar, DIG Frank Mba ya jagoranci fitar da gwamnan daga cikin ofishin hukumar tun cikin asubahin yau Lahadi.
Bayanai sun ce gwamnan ya je cibiyar tattara sakamakon ne domin bayyana ƙorafinsa kan zargin aikata ba daidai ba a sakamakon wasu ƙananan hukumomin jihar ciki har da ƙaramar hukumarsa ta Oredo.
Daga nan ne kuma jami’an ‘yansanda ƙarƙashin jagorancin DIG Mba da wasu jami’an soji suka isa cibiyar domin fito da gwamnan.
Jam’iyyar APC mai hamayya dai ta yi ƙorafi kan zuwan gwamnan cibiyar tattara sakamakon.
Nan gaba kaɗan ne hukumar zaɓen za ta fara aikin tattara sakamakon zaɓen daga ƙananna hukumomin jihar 18.
BBC Hausa