Yanayin Ruwan Sama Ne Ya Janyo Jinkiri Wajen Tattara Sakamakon Zaben Jihar Edo
Daga Shafin BBC Hausa
An shafe daren jiya ana dakon fara tattara sakamakon zaben jihar Edo inda hukumar ta INEC ta ce har zuwa karfe biyu na daren Asabar din da aka yi zaben, babu karamar hukuma guda da ta isa cibiyar tattara sakamkon zabe da ke birnin na Benin.
Kodayake mai magana da yawun hukumar zaben Najeriya INEC, Hajiya Zainab Aminu, ta shaida wa BBC cewa tun da farko an fara samun matsala ce sakamakon ruwan sama da aka wayi gari dashi abin da ya janyo tsaiko wajen kai kayayyakin zaben da ma’aikata wasu mazabun.
Ta ce hakan ya sa an dan samu jinkiri wajen kada kuri’a a wasu wuraren.
Hajiya Zainab, ta ce “ Jinkirin fara kada kuri’a da wuri a wasu wuraren ya sa tattara sakamakon zaben ma ya samu jinkiri.”
Ta ce,” Baya ga jinkirin kai kayan zabe, rashin kyawun hanyoyin zuwa wasu garuruwa ma ya kara haifar da jinkiri, ballantana ga damuna kuma.
A bangare guda kuma, manyan jam’iyyun adawa a zaben gwamna a jihar ta Edo, wato PDP da APC, sun fara nunawa juna yatsa, inda kowannesu ke zargin an tafka magudi a zaben da aka yi a ranar Asabar.
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa an sauya sakamakon zaben wasu rumfuna abin da hukumar zabe ta INEC ta bayyana shirin gudanar da bincike a kai.
Kwamishinan zaben jihar Anugbum Onuoha, ya bayar da tabbacin yin aiki da gaskiya wajen tabbaar da duk dan takarar da ya samu nasara.
An dai gudanar da zaɓen ne cikin tsaurarn matakan tsaro a ƙananan hukumomi 18, sai dai ba a samu fitar jama’a da dama a wuraren jefa kuri’a.
A cikin daren jiya hukumar zaben ta tura fiye da kashi casa’in cikin dari na sakamakon a matakin rumfuna ta intanet na kimanin rumfuna 4,082 daga cikin rumfuna 4,519 da ke akwai a fadin jihar.