DA ƊUMI-ƊUMI:🔥 Ƴan sa-kai sun hallaka ƙasurgumin ɗan bindiga da jama’arsa a Zamfara
Daga Shafin Sahel24 TV
Wasu ƴan sa-kai da suka sadaukar da kansu wajen yaƙi da ƴan bindigar da suka addabi jihar Zamfara sun samu nasarar hallaka wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi yankin Ɗansadau da ke ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.
Ɗan bindigar mai suna Black, yau ya gamu da ajalinsa ne shi da tawagarsa bayan da wasu jajirtattun matasa suka yi masa kwanton ɓauna shi da tawagarsa a kan hayarsu ta zuwa wajen aika-aika.
Wani mazaunin yankin da muka sakaya sunansa ya tabbatar wa Sahel24 Tv cewa, “Matasan gari ne suka ji labarin ɗan bindigar da tawagarsa zai wuce sai suka masa kwanton ɓauna a lokacin da suke kan babura biyar kuma suka samu nasarar hallaka su duka” in ji shi a yayin zantawar mu da shi ta wayar salula.
Lamarin dai ya faru ne a ƙauyen Ƴartashar Sahabi da ke yankin Ɗansadau a ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
Wannan nasara dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da jami’an sojin Najeriya suka yi nasarar hallaka ƙasurgumin ɗan bindiga Halilu Sububu duk a jihar ta Zamfara da ta daɗe tana fama da ayyukan ta’addanci.