Labaran Duniya

Gwamnatin Kaduna Ta Tabbatar Da Mutuwar @Danta’adda Kachalla Tukur Sharme

Gwamnatin jihar Kaduna a arewacin Najeriya ta ce an kashe jagoran ‘yanfashin daji Kachalla Tukur Sharme yayin wata musayar wuta tsakaninsa da abokan gaba.

Kwamashinan Tsaro Samuel Aruwan ya faɗa cikin wata sanarwa cewa an kashe Sharme ne tare da wasu ‘yanbindiga biyu yayin musayar wutar da ta kai ga kuɓutar da wasu mutane da aka yi garkuwa da su.

Shi ne ya jagoranci sace ɗaliba 121 na sakandaren Bethel Baptist High School ranar 5 ga watan Yulin 2021, a cewar kwamashinan.

Ya ƙara da cewa da yawa daga cikin mambobin ɓangarorin sun tsere da “muggan raunuka a jikinsu” bayan fafatawar da suka yi a ƙarshen mako, kamar yadda majiyoyin tsaro suka tabbatar musu.

Sun far wa juna ne a yankin Hambakko da ke tsakanin Rijana da dajin Kaso, in ji kwamashinan, yana mai cewa Sharme ya tsallake rijiya da baya a hannun jami’an tsaro.

“Sharme da sauran abokan hulɗrsa sun sha gudanar da ayyukansu a yankunan Maraban Rido, Kujama, Kajuru, Maro…ƙari a kan ta’addancin da yake yi a jihohin Katsina da Neja.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button