Rundunar Sojin Najeriya Ta Hallaka Mayaƙan Boko Haram 23 A Jihar Borno
Daga Shafin Sahel24 TV
Dakarun sashe na 3 na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Ƙasa da Ƙasa (MNJTF) sun yi nasarar kashe ’yan ta’addan Boko Haram 23 a Jihar Borno.
Aminiya ta ruwaito cewa, fafatawar ta faru ne a ranar Lahadi, 23 ga watan Satumba, a kusa da Malam Fatori, bayan wata arangama inda sojoji suka daƙile wani harin da maharan suka kai musu.
A cewar masanin harkokin tsaron nan a tafkin Chadi Zagazola Makama, sojojin sun yi wa mayaƙan na ISWAP kwanton ɓauna, inda suka yi ta harbe-harbe da ya yi sanadin mutuwar ’yan ta’adda 23 wasu da yawa kuma suka tsira da munanan raunuka.
A cewarsa, a yayin fafatawar wasu sojojin Najeriya biyu suka samu raunuka, amma ba a samu asarar rai ba a cikin sojojin.
Haka nan dakarun na MNJTF sun kwato makamai masu yawa daga hannun ’yan ta’addan da suka haɗa da bindiga ƙirar PKM, bindiga AK-47, gurneti da harsasai masu tarin yawa.