Iftila’i: Hatsarin kwale-kwale ya ci rayuka 4 a Borno
An tabbar da rasuwar aƙalla mutane huɗu sakamakon kifewar wani kwalekwale a Karamar Hukumar Dikwa da ke Jihar Borno.
Aminiya ta ruwaito, kakakin ’yan sanda a jihar, ASP Kenneth Daso, ya sanar a ranar Talata, cewa “hatsarin kwale-kwalen ya afku a ranar 23 ga watan Satumba 2024, a yankin Bakassi da ke tsakanin Mafa da Dikwa a kan hanyar Maiduguri, inda ya yi sanadin asarar rayukan mata hudu.
“Wadanda suka mutu, dukkansu ’yan unguwar Bulabulin, Dikwa, kuma an gano su, an kai su babban asibitin Dikwa, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.
“Daga bisani an mika gawarwakin ga iyalansu domin yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.”
Kwamishinan ’yan sandan jihar, ML Yusufu, a yayin jajantawa, ya bukaci mazauna yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa, da su yi taka-tsan-tsan a wannan lokaci, tare da gaggauta kai rahoton duk wani lamari na gaggawa.