Shugaba Tinubu Zai Chanja Ministocin Kasar Nan Bada Jimawa Ba
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa zai yi wa majalisar ministocinsa kwaskwarima nan gaba kaɗan, a cewar mai magana da yawunsa Bayo Onanuga.
“Shugaban ƙasa ya ce zai yi wa majalisarsa kwaskwarima. Ban sani ba ko zai yi hakan kafin 1 ga watan Oktoba amma dai tabbas zai yi […] bai faɗa mana lokaci ba dai” in ji shi lokacin da yake magana da manema labarai a yau Laraba.
Mista Onanuga ya ce shugaban ya kuma umarci ministcin “da su daina jin kunyar yin magana da kafofin yaɗa labarai” domin tallata ayyukan gwamnatin.
A cewarsa: “Wasu daga cikinsu na gudun magana a talabijin, ko rediyo. Ya nemi su daina yin hakan, su fita su bayyana ayyukan da suke yi.”
Babu tabbas game da dalilin da ya sa Tinubun zai yi sauyin a daidai wannan lokaci. Akasarin ministocin gwamnatin Muhammadu Buhari – wanda Tinubu ya gada – sun shafe kusan shekara takwas a kan mulki.