Rahotanni A Jamhuriyar Benin Na Cewa Hukomomi Sun Kama Mutun Uku Akan Zargin Shirin Juyin Mulki A Kasar
Hukomomi sun kama mutum uku bisa zarginsu da Shirin juyin mulki a Jamhuriyar Benin, kamar yadda aka bayyana.
Kamar yadda mai gabatar da ƙara, tsohon Ministan Wasanni, Oswad Homeky da ɗankasuwa kuma tsohon abokin shugaban ƙasa Patrice Talon mai suna Olivier Boko da kwamandan sojoji masu kula da shugaban ƙsa wato Republican Guard ne kan gaba wajen kitsa juyin mulkin.
Mai gabatar da ƙarar ya ce an kama tsohon ministan a lokacin da “yake mika wa kwamandan askwaran jakunkuna guda shida cike da tsabar kuɗi.”
Masu binciken sun ce sun gano Homeky da Boko sun ba kwamandan sojin waɗanda alhakin kula da shugaban ƙasa ya rataya a kansu domin su kawar da kansu idan ana gudanar da juyin mulkin da aka shirya gudanarwa a ranar 27 ga Satumba.
Ana kuma zargin Homeky da Boko sun samu haɗin gwiwar wasu jami’an tsaro, waɗanda ake cigaba da bincike domin gano su.
A kwanakin baya ne Boko ya sanar da ƙudurinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a shekarar 2026, lokacin wa’adin zango na biyu na mulkin Talon zai ƙare.