Wasanni

Kotu Ta Tura Wanda Ya Zagi Chukwueze Da Vinicius Jr Gidan Yari Na Tsawon Shekara Daya.

Kotu ta samu wani masoyin Mallorca da laifin zagin launin fatar ɗan wasan gaba na Real Madrid, Vinicius Jr ɗan asalin Brazil, da kuma ɗan wasan Villarreal Samuel Chukwueze, ɗan asalin Nijeriya.

Zagin da aka yi wa Vinicius da Chukwueze sun faru ne makonni biyu tsakani, a wasanni biyu da aka buga bara, a filin wasa na Son Moix na birnin Palma da ƙungiyar Mallorca take.

An jiyo masoya ƙwallo a yayin wasan Mallorca da Real Madrid suna kiran ɗan wasan na Brazil da biri. Kuma da ma Vinicius yana yawan koke kan a yaƙi wariyar launin fata a wasan ƙwallo a Sifaniya.

Sai a yanzu ne kotu ta kama mai laifin dumu-dumu, inda zai yi zaman gidan kaso na tsawon shekara guda. Baya ga ɗauri, an kuma haramta wa mutumin shiga filayen wasa na tsawon shekaru uku.

Real Madrid ta sanar yau Alhamis cewa mai laifin, wanda ba a ambaci sunansa ba, za a jinkirta wa’adin ɗaurin nasa na watanni 12, bayan da ya ba da haƙuri cikin wata wasiƙa da ya rubuta wa Vinicius, kuma ya shiga shirin horon kan yaƙi da wariyar launin fata.

Sanarwar ta Madrid ta ce, “Wannan ne karo na uku da ake kama wani da laifin a ‘yan watannin nan, sakamakon zagin launin fatar wani ɗan wasan Real Madrid”.

Ƙungiyar ta Real Madrid ta sha alwashin ci gaba da yaƙi don kare manufofin ƙungiyar don kawar da halayyar wariyar launin fata a duniyar ƙwallo da ma wasanni gabaɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button