Matar Gwamnan Jihar Akwa Ibom Ta Rasu
A Cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ini Ememobong ya fitar, a yau Juma’a ya ce ta mutu ne tun a jiya ranar Alhamis.
Sanarwar ta ƙara da cewa marigayiyar ta rasu ne a gaban iyalai da danginta.
An dai haifi Patience ne a garin Ikot Akpa Ekop da ke yankin Ikpa Ibom, yankin ƙabilar Mkpat Enin da ta yi fice wajen noma kwakwan manja da sarrafa shi.
Marigayiyar da gwamnan na Akwa Ibom sun yi shekara 37 suna tare a matsayin mata da miji kamar yadda jaridar The Nation ta bayyana, inda suka haifa yara shida da jikoki tara.
Ita ce ta assasa gidauniyar Golden Initiative For Alla (GIFA) domin ayyukan jin ƙai da taimakon marasa galihu, inda ta yi amfani da gidauniyar wajen gina rijiyoyin burtsatse da tallafa wa mata masu shayarwa da wayar musu da kai da taimakon ilimin yara marasa galihu da ciyar da su da sauransu.