Labaran Duniya

Wani Kasurgumin Dan Boko Haram Ya Mika Wuya Ga Sojojin Najeriya

Daga Shafin BBC Hausa

Rundunar dakarun ƙasashen da ke yaƙi da ƙungiyar Boko Haram ta MNJTF, ta ce wani kasurgumin ɗan Boko Haram, mai suna Bochu Abacha, ya miƙa wuya ga sojojin Najeriya da ke aiki a karamar hukumar Kukawa na jihar Borno.

Jami’in yaɗa labarai na rundunar a Ndjamena, Laftanar Kanar Olaniyi Osaba ne ya bayyana haka ga manema labarai a Maidguri ranar Asabar.

Osaba ya ce Abacha, wanda ya kasance yana da hannu a kai hare-hare da dama, ya amsa shiga gaba wajen kai hare-hare a kan hanyar Mongunu zuwa Baga.

“Abacha ya miƙa wuya ne sakamakon zafafan farmaki da MNJTF ke kai wa da kuma buƙatarsa ta son ganin an samu zaman lafiya,” in ji Osaba kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.

Ya ce ɗan Boko Haram ɗin ya kuma miƙa bindiga AK 47 ɗaya cike da harsasai da wayar salula da layin wayar kamfanin Airtel da kuma kuɗi N32,500.

Jami’in ya ce wanda ake zargin na bai wa hukumomi bayan sirri da zai taimaka musu a aiki.

A ɗaya gefen, rundunar MNJTF tare da haɗin gwiwar wasu jami’ai sun yi wasu mayakan Boko Haram kwantan ɓauna tare da kashe ɗaya daga cikinsu.

Dakarun sun yi artabu da mayakan, inda daga bisani wasu suka samu damar tserewa har da barin makamansu.

Osaba ya ce sun gano motoci uku ɗauke da kayan abinci da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button