Rahotanni
‘Yan bindiga sunyi garkuwa da mutane 5 a Ƙaura Namoda.
Da misalin karfe 2 na daren jiya Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kutsa kai a sabon garin kaura Namoda inda nan take sukayi garkuwa da Maza 4 mace 1.
Lamarin ya zo ne bazace duba da yanda cikin kwanukan nan ake samun nasara a yaƙi da jami’an tsaro ke yi harkar ta’addanci a arewa maso yammacin kasar nan.
Kawo rubuta wannan labari babu wani bayani daga hukumomin tsaron Yankin.
Sahel24 TV