Labaran Duniya

Zaratan Dakarun MNJTF Sunyi Nasarar Dakile Harin Boko Haram A Jihar Borno

Dakarun rundunar ƙawance ta Multinational Joint Task Force (MNJTF) sun yi nasarar daƙile wani hari da Boko Haram ta yi aniyar kaiwa a jihar Borno, a cewar rundunar cikin wata sanarwa ranar Asabar.

Kakakin rundunar, Laftana Kanal Olaniyi Osoba, ya ce bayanan sirri sun nuna mata cewa mayaƙan ƙungiyar na shirin kai harin ne a yankin Magumeri zuwa Maiduguri.

Ganin haka ne ya sa dakarun suka ƙaddamar da harin ba-zata, inda suka yi wa maharan kwanton ɓauna.

“Wannan yunƙurin ya sa dole suka haƙura da kai harin kuma suka zubar da makamai da baburan da suke kai kafin su haddasa fitina a yankin.” in ji kanar ɗin.

Osoba ya ƙara da cewa sojojin sun karaɗe yankin bayan ɓarin wutar da suka yi kuma suka gano bindigogi ƙirar AK-47, da jakar harsasai 51, da miyagun ƙwayoyi daban-daban da ‘yanbindigar suka gudu suka bari.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button