Labaran Duniya

Anyi Nasarar Ceto Yara 19 Yan Asalin Jihar Kebbi Da Akayi Safarar Su Zuwa Jihar Cross River

Gwamnatin jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya ta ce ta yi farin ciki da nasarar da aka samu ta ceto wasu yara 19, ƴan asalin jihar da masu fasaƙaurin mutane suka sace suka kai su Cross River da ke kudancin ƙasar.

Gwamnan jihar Kwamred Nasir Idris ne ya bayyana haka yayin bikin karɓar yaran da aka yi a gidan gwamnatin jihar da ke Birnin Kebbi, tare da shan alwashin ƙin amince wa da irin wannan al’ada ta safarar mutane a jiharsa.

A cewar gwamna Nasir Idris, an samu nasarar ƙwato yaran ne da haɗin gwiwar hukumar NAPTIP mai hana fasaƙaurin mutane.

Ya ce yaran waɗanda adadinsu ya kai 19 dukkansu babu wanda ya wuce shekara 11.

Gwamnan ya ƙara da cewa hukumar NAPTIP ta bibiya labarin sannan ta sanar da gwamnati inda kuma suka yi tattaki zuwa birnin Calabar tare da gano yaran da wanda ake zargi da jagorancin safarar yara a jihar.

“Abin baƙin ciki, bincike da hukumar lafiya ta yi a asibiti ya nuna cewa ana kwana da ƙananan yaran ƴan shekara 10 zuwa ƙasa, wannan ba al’adar mu ba ce.” in ji gwamna Nasir Idris.

Gwamnan Nasir Idris ya ci gaba da cewa iyaye da dama na sakaci suna ba da yaransu da sunan za a kai su makaranta, sai dai saɓanin haka ne ke faruwa da yaran.

Ya kuma ce kowanne mahaifi ya sani abin tambaya ne ga kiwon yayansa da ubangiji ya bashi a matsayin kyauta.

Najeriya na daga cikin ƙasashen da ke fama da masu fasaƙaurin mutane na cikin gida da kuma na ƙetare.

Ko a ƙarshen makon jiya sai da hukumar NAPTIP ta miƙa wasu yan mata takwas ‘yan Najeriya da aka yi fasaƙaurinsu zuwa ƙasar Ghana ga iyayensu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button