Labaran Duniya

Matar da ta auri kan ta ta yi murnar cika shekara ɗaya da bikin auren ta

Daga Shafin Sahel24 TV

Ƴar Birtaniya da ta auri kan ta, ta kuma yi bikin aure na na kasaita sakamakon rashin samun wanda zauciyarta ta kwanta da shi, ta yi bikin cikarta shekara ta farko a dakin aure.

Sarah Wilkinson, mai shekara 43, ta gudanar da bikin auren a Grade II-listed Harvest House in Felixstowe, Suffolk, a ranar 30 ga Satumba.

Ta yi bikin ne a gaban abokai da yan uwa kusan 40.

Wilkinson ta ce ta shirya bikin ne domin nuna cewa za ta iya zama ita kadai a rayuwa, inda ta ce “ina jin dadin zama a hakan; ba lallai ne sai ka zauna da wani za ka samu cikakkiyar rayuwa ba”.

Ba zan ce bana son zama da kowa ba, idan hakan ta faru ba damuwa, to abin mamaki, idan kuma bai faru ba, hakan ma daidai ne,” in ji ta.

Ta ci gaba da bikin inda ta kashe fan dubu 10,000 inda ta ce “ba a yi ni dan ina son miji, gida, yara ba, amma rayuwa ba ko yaushe ta ke kasance wa haka ba kuma in hakan ta samu ma daidai ne”.

Wilkinson ta yi bikin murnar zagayowar ranar ne ta hanyar aikewa da kanta fulawa da lemuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button