Kotu A Najeriya Ta Haramtawa Jami’an Hukumar VIO Kama Masu Ababen Hawa Da Kuma Cin Tara
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja babban birnin tarayyar Najeriya ta haramta wa hukumar bincike da kula da zirga-zirgar ababen hawa kwacewa ko kuma tarar masu ababen hawa.
Alkaliyar kotun da ta zartar da hukuncin mai shari’a Nkeonye Maha ta ce babu wata doka da ta ba VIO damar tsayarwa ko kamawa da cin tarar ababen hawa.
Wani lauya Abubakar Marshal ne mai rajin kare haƙƙin ɗan’adam ya shigar da ƙarar. Kuma kotun ta saurari kokensa inda hukuncin kotun ya ce “cin tarar ko wane irin abun hawa bai dace ba kuma ya saɓa doka.
Kotun ta kuma yi umarnin hana duk wani mai aiki da yawun VIO ci gaba da keta haƙƙin ƴan Najeriya da ƴancinsu na walwala.
“Kotu ce kawai ke da ƴancin saka tara kan abun hawa da aka kama da saɓa doka,” a cewar alƙaliyar kotun.
Sannan ta ƙara cewa hukumar da ke ƙarƙashin ikon ministan Abuja babu wata doka da ta ba su damar tsayarwa da kamawa ababen hawa tare da cin su tara.