Labaran Duniya

Jami’an hukumar Yan sanda sun bayyana dalilinsu na tura Karin Jami’an tsaro a Fadar Sarki  Sanusi II da Sarki Aminu Ado Bayero

 Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta fito ta yi magana kan dalilin da ya sanya aka ga ƙarin jami’an tsaro a fadar Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero

 Kwamishinan ƴan sandan jihar mai barin gado, AIG Usaini Gumel, ya bayyana cewa an tura ƙarin jami’an tsaron ne domin samar da tsaro a wuraren guda biyu Ya bayyana cewa jami’an tsaron an tura su ne domin tabbatar da zaman lafiya har zuwa lokacin da za a kawo ƙarshen rikicin na masarautar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button