Labaran Duniya
Dan majalisar tarayya a jihar Zamfara zai gudanar da Auren marayu
A cikin Shirin bukukuwan cikar sa shekara daya a Kan karagar mulkin kananan hukumomin Bungudu da Maru a Majalisar tarayya ta Najeriya Hon. Dr Abdulmalik Zubairu Bungudu yace, sun shirya tsab domin gudanar da auren Marayu ‘yayan wadanda suka riga mu gidan gaskiya a sakamakon hare-haren yan bindiga.
A kalla dai kimanin Marayu 105 ne da aka zakulo daga mazabu 21 na kananan Hukumomin guda biyu na Bungudu da Maru zasu ci gajiyar wannan shirin.
Haka zalika ya Kara da cewa zasu gudanar da taron “Jin Ra’ayoyin Jama’a” wato (Special Maiden Town Hall Meeting) akan wannan dama da Allah Ya basu domin lalubo hanyoyin cigaba da inganta wakilcin da suke yi da yardar Allah.