Labaran Duniya

Jami’an hukumar Yan sanda sun tabbatar da garkuwa da akayi da Alkalin Babbar Kotun tarayya

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno suntabbatar da yin garkuwa da Alkalin Babbar Kotun Tarayya, Mai shari’a Haruna Mshelia, da matarsa, da kuma Odilii da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi a kauyen Gujba dake Jihar Yobe.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, PPRO, ASP Kenneth Nahum Daso, ya kuma tabbatar da cewa motoci biyu cike da fasinjoji da aka sace a hanyar Damaturu zuwa Kamuya dake kan titin Buratai.

A cewar PPRO, an kafa wata tawagar hadin gwiwa ta jami’an tsaro da za ta bi diddigin mutanen da aka sace tare da kubutar da su. 

Rundunar ta bukaci jama’a da su bayar da duk wani bayani mai amfani da zai taimaka wajen gudanar da bincike domin ceto su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button