Kungiyar kwallon kafa ta PSG na tunanin zawarcin dan wasan Manchester United Marcos Rashford, yayin da Chelsea ke zawarcin Lucy Bronze.
Paris St-Germain za ta yi tunanin zawarcin dan wasan gaban Manchester United Marcus Rashford kuma za ta iya zage dantse idan ta samu kwarin gwiwa cewa dan wasan na Ingila mai shekara 26 a shirye yake ya koma kungiyar.
Manchester City ta gaza kawo cikas ga yunkurin Bayern Munich na daukar dan wasa Michael Olise mai shekaru 22 daga Crystal Palace.
Chelsea na son dan wasan bayan Nottingham Forest dan kasar Brazil, Murillo, mai shekara 21, wanda City Ground ta sanya farashinsa a kan fan miliyan 70, kuma za ta iya bayar da dan wasan bayan Ingila Trevoh Chalobah, mai shekara 24, a matsayin wani bangare na duk wata yarjejeniya.
Chelsea ta tuntubi Leicester City game da sayen dan wasan tsakiyar Ingila Kiernan Dewsbury-Hall, mai shekara 25, wanda aka fahimci yana son komawa Blues ne kawai idan ya bar Foxes.
Aston Villa ta ki amincewa da tayin fam miliyan 20 daga Tottenham kan dan wasan tsakiya na Ingila Jacob Ramsey, mai shekara 23, a yarjejeniyar da ta shafi dan wasan tsakiya na Argentina Giovani lo Celso, mai shekara 28.
Napoli ba ta da niyyar siyar da dan wasan gaba na Georgia Khvicha Kvaratskhelia a wannan bazarar.
AC Milan ta shaida wa Newcastle cewa sai ta tanadi kudi kusan fam miliyan 40 don daukar dan wasan bayan Ingila Fikayo Tomori mai shekaru 26 daga San Siro.
Dan wasan tsakiya na Arsenal dan kasar Belgium Albert Sambi Lokonga, mai shekara 24, ya amince da yarjejeniyar sirri da Sevilla domin ya koma kulob din na Spain a matsayin aro na kakar wasa.