Jam’iyar APC A Zamfara Ta Gudanar Da Wani Muhimmin Taro A Gusau
A yau Assabar ne Jam’iyar APC a Gusau Babban birnin jihar Zamfara ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki tun bayan nada sabbin shuwagabannin kungiyar tsawon shekara daya.
Taron dai ya hada da dukkanin bangarora guda biyu na jagororin Jam’iyyar Apcn ta Zamfara Hon Bello Matawallen Maradun, da takwaran sa Sanata Mai Wakiltar Zamfara ta Yamma, Hon Dr. Abdulaziz Yari Abubakar, Shattiman Zamfara.
Dukkanin bngaroran Sunyi Jawabi tare da Jinjinama Jagororin bisa Kulawa da Kuma Taimako da Sukema Ya’yan Wannann Jam’iyya ta Apc Mai Albarka, Wanda Suka Bayyana Cewa Jam’iyyar Ta Soma Wannann Zama Kenan Na Lokaci Bayan Lokaci Domin Karfafawa da Kuma Karama Ya’yan Jam’iyyar Kwarin Gwaiwa Domin Zaman Jam’iyyar Tsintsiya Madaurinki Daya.
Taron Ya samu Halartar Shugaban Jam’iyyar Apc Na Jahar Zamfara, Alh Tukur danfulani Mai Katako, da Shugaban Jam’iyyar Na Gusau, Alh Tijjani Dan Ayya, Da Tsohon Shugaban Karamar Hukumar mulkin Gusau, Engr Babangida️️️ Abdullahi Zannan Damba, Sai Alh Sanusi Sarki, Tsohon Kantoman Gusau, da Sauran Muhimman Mutane.