Cutar Kwalara ta Bulla a gidan yarin Kirikiri dake Legas
Kwamishinan lafiya na jihar Legas ya bayyana cewa an samu mutum 25 waɗanda suka kamu da kwalara a gidan yari na Kirkiri da ke jihar.
Wannan na zuwa ne bayan a makon da ya gabata, hukumar kula da gidajen gyara hali na ƙasar ta bayyana cewa babu ɓullar cutar a gidajen yarin ƙasar.
Sai dai a jiya Lahadi, wata sanarwa da ta samu sa hannun darakatan yada labarai na ma’aikatar lafiya ta jihar Legas, Tunbosun Ogunbanwo ta ce an samu “ƙwarya-ƙwaryar ɓarkewar kwalara ta mutum 25 wadanda suka koka kan mummunan ciwon ciki.”
Sai dai sanarwar ta ce an ɗauki mataki na gaggawa wajen shawo kan lamarin.
Kwalara dai cuta ce wadda ke iya kashe mutum cikin ƙanƙanin lokaci matuƙar ba a ɗauki matakan da suka dace a kan lokaci ba.
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta Najeriya ta ce mutum 53 ne suka mutu ya zuwa watan Yunin 2024 sanadiyyar yaɗuwar cutar a faɗin ƙasar.