Kotun dake sauraren Karar Tsohon Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ta dage Ranar yanke Masa Hukunci
Alƙalin wata kotun birnin New York ya jinkirta bayyana hukunci kan tsohon Shugaban Amurka Donald Trump bayan lauyoyinsa sun nemi ɗaukaka ƙara biyo bayan hukuncin kotun ƙoli.
Tun da farko an tsara yanke wa Trump hukunci ranar 11 ga watan Yuli game da zargin biyan wata ‘yar fim ɗin batsa kuɗaɗe domin ta rufa masa asiri.
Tawagar lauyoyinsa sun nemi a sauya hukuncin kotun ne bayan Kotun Ƙolin Amurka ta yi hukunci a ranar Litinin cewa tsohon shugaban na da kariya daga wasu tuhume-tuhume bisa ayyukan da ya gudanar “a hukumance” lokacin da yake shugaban ƙasa.
Mai Shari’a Juan Merchan ya ce zai sanar da matakin da ya ɗauka kan lamarin nan da 6 ga watan Satumba.
Ya ƙara da cewa idan idan ya zama dole a yanke masa hukunci to za a yi hakan a ranar 18 ga watan na Satumba.
A ranar 30 ga watan Mayu ne kotun ta kama Trump da laifin aikata tuhuma 34 da ake yi masa da suka shafi yin ƙarya a takardun bayanan kasuwancinsa da zimmar ɓoye kuɗaɗen da ya biya ‘yar fim ɗin batsar mai suna Stormy Daniels.