Kamfanin Mai na Nijeriya NNPCL Ya Kaddamar Da Dokar ta Baci A Kan Hako Danyen Man Fetur
Kamfanin Man Nijeriya NNPCL ya ƙaddamar da dokar ta ɓaci a kan haƙar ɗanyen mai don ƙara yawan abin da ake haƙowa da inganta abin da ake adanawa.
Shugaban kamfanin Malam Mele Kyari ne ya bayyana haka a Abuja ranar Talata, lokacin da yake jawabi a wajen wani taro kan man fetur da iskar gas.
Mele Kyari ya ce “Mun yanke hukunci dakatar da ce-ce-ku-ce. Mun ƙaddamar da yaƙi kan ƙalubalen da ke addabar harkar samar da ɗanyen manmu.
“Yaƙi yana nufin yaƙi. Muna da abubuwan da suka dace, mun kuma san yadda za mu yi yaƙin,” a cewarsa.
Kamfanin mai na NNPCL ya tabbatar da sauya farashin fetur a Nijeriya
Ya ce cikakken nazarin da suka yi kan kayan aikin kamfanin ya nuna cewa za a iya haƙo ɗanyen mai ganga miliyan biyu a kowace rana ba tare da sanya sababbin injinan haƙo man ba. Sai dai ya ce babban abin da ke kawo musu matsalar cim ma hakan shi ne yadda masu ruwa da tsaki ba sa aiki a kan lokaci.
Shugaban na NNPCL ya bayyana cewa kamfanin ya san duk abin da ya kamata ya yi a kowane mataki, ya kuma ƙara da cewa suna aiki da dukkan abokan hulɗarsu. Ya ce za su yi aiki tare don inganta yanayin da ake ciki.
Mele Kyari ya ƙara da cewa “yaƙin zai taimaki NNPCL da abokan hulɗarsa su yi gaggawar kawar da duka wasu matsaloli da aka gano, waɗanda su ne suka dabaibaye harkar haƙo man yadda ya kamata, kamar jinkiri wajen sayo kayan aiki.”
Ya kuma bayyana cewa, a matakan matsakaici da dogon zango, kamfanin NNPCL zai sauya tsofaffin butun ɗanyen mai da suka shafe fiye da shekaru 40 ana amfani da su.