Kungiyar Hamas ta ce ta mayar da martani mai kyau ga Isra’ila kan shirin zaman lafiya na Biden
Wani jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa, kungiyarsa ta mayar da martani mai kyau ga sabon kudurin tsagaita wuta a Zirin Gaza tare da sanar da masu shiga tsakani cewa a shirye suke da duk wata shawara da ta dace da bukatun al’ummar Falasdinu.
Ali Baraka shugaban sashen hulda da jama’a na Hamas da ke kasashen waje ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Anadolu cewa, bangarorin Hamas da Falasdinawa a shirye suke ga duk wani shiri da zai biya bukatun al’ummarFalasdinu.
A cewar Baraka, bukatun al’ummar Falasdinu sun hada da “tsagaita wuta na dindindin, da janyewar sojojin Isra’ila daga Zirin Gaza gaba daya, da mayar da mutanen da suka rasa matsugunansu zuwa gidajensu, da samar da agaji, da kuma fara aikin sake gina kasar.”
Jami’in Hamas ya ce “Idan har sabon shirin ya kawo karshen ta’addancin da ake yi wa al’ummar Falasdinu da kuma janyewar sojojin mamaya, za mu mayar da martani mai kyau a kansa.”
Kamfanin dillancin labaran WAFA na kasar Falasdinu ya bayar da rahoton cewa, Falasdinawa da dama sun shaƙe da hayaƙi mai sa hawaye da sojojin Isra’ila suka fesa a garin Beita da ke kudancin Nablus a Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.
Rahoton ya ce sojoji sun harba bama-bamai da robobin iskar gas kan matasan yankin, lamarin da ya sa da dama daga cikinsu shaƙe da hayaƙi saboda shaƙar iskar gas.
Isra’ila ta kashe Falasdinawa akalla 10 tare da raunata wasu da dama ciki har da yara ƙanana, bayan da ta kai hari a wurare da dama a Gaza da aka yi wa ƙawanya.
Majiyoyi sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na WAFA cewa an kashe mutane biyu a Khan Younis, hudu a sansanin Nuseirat, hudu kuma a unguwar Daraj.