Akalla Gawarwakin Falasɗinawa 10 ne Aka Tono A ƙarƙashin Wasu Baraguzai a kudancin Gaza
An kwaso gawarwakin Falasdinawa akalla 14 daga ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da ke Rafah a kudancin Zirin Gaza, kamar yadda majiyoyin lafiya suka shaida wa Anadolu a ranar Juma’a.
Majiyar ta ce sun karbi gawarwakin Falasdinawa 14 daga yankunan yammacin birnin Rafah da ke kudancin Zirin Gaza.
Majiyoyin kiwon lafiya sun kara da cewa akalla guda 10 daga cikin wadancan gawarwakin sun ruɓe ne kuma ba a tantance su ba.
Isra’ila, wadda ta yi fatali da kudurin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya bukaci a tsagaita wuta cikin gaggawa, ta fuskanci tofin Allah tsine daga kasashen duniya a daidai lokacin da take ci gaba da kai munanan hare-hare kan Gaza tun bayan harin da kungiyar Hamas ta Falasdinu ta kai a ranar 7 ga Oktoba, 2023.
Fiye da Falasdinawan 38,000 ne aka kashe tun daga lokacin, akasari mata da yara, yayin da wasu sama da 87,000 suka jikkata, a cewar hukumomin lafiya na yankin.
Kusan watanni tara da fara yakin Isra’ila, yankunan Gaza da dama sun koma kufai a cikin yanayi na takunkuman da aka sanya wa zirin na hana shigar da abinci da ruwa mai tsafta da kuma magunguna.
Ana tuhumar Isra’ila da aikata kisan kiyashi a kotun kasa da kasa, hukuncin da aka yanke na baya-bayan nan ya ba da umarnin dakatar da aikin soji a kudancin birnin Rafah, inda Falasdinawa sama da miliyan guda suka nemi mafaka daga yakin kafin a mamaye shi a ranar 6 ga watan Mayu.