Labaran Duniya

An samu fitowar Al’uma masu zaɓe sosai a zagaye na biyu na zaɓen Faransa

Mutane sun fito sosai domin kaɗa ƙuri’a a zagaye na biyu na zaɓen majalisar dokokin Faransa.

An dai yi hasashen cewa zaɓen zai kafa tarihi a matsayin wanda aka fi samun fitar masu kaɗa ƙuri’a a cikin shekara 40.

Fiye da kashi 85 na Kujeru Majalisar dokokin ne ake takara a kansu.

Ana gudanar da zaɓen ne cikin tsauraran matakan tsaro saboda irin yaƙin neman zaɓen da aka gani, inda wasu ƴan takarar suka riƙa kai wa juna hari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button