Labaran Duniya
Dakarun Kasar Isra’ila Sun kashe wani babban jami’in Hamas a Gaza
Harin da Isra’ila ta kai kan wata makaranta a birnin Gaza ya kashe wani babban jami’in ƙungiyar Hamas.
Kafar yaɗa labaran Hamas ta ce an kashe Ehab al-Ghussein tare da wasu mutum uku a hari kan makarantar da ɗaruruwan Falasɗinawa ke neman mafaka a cikinta.
Ehab al-Ghussein shi ne tsohon kakakin ma’aikatar cikin gida na Hamas, inda a baya-bayan nan kuma ya riƙe muƙamin mataimakin mistan ƙwadago.
Rahotonni sun ce harin ya faɗa kan wasu azuzuwa biyu a makarantar.
Sojojin Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare a faɗin Gaza, yayin da ƙungiyar Hezbollah ke ci gaba da kai hare-haren rokoki kan iyakar arewacin Isra’ilar.