Labaran Duniya

Majalisar Wakilai Ta Yi Watsi Da Yarjejeniyar SAMOA Da Gwamnatin Tarayya Ta Rattabawa Hannu

Majalisar Tarayya ta yi wa Gwamnatin Tarayya kakkausan kiran cewa ta dakatar da fara aiki da duk wata yarjejeniyar da ke ƙunshe cikin Yarjejeniyar Samoa, wadda ake zargin akwai ɗaure wa baɗala da ‘yan halasta “LGBTQ+ a ciki.”

Haka nan kuma majalisa ta umarci Kwamitin Tsare-tsaren Ƙasa ya binciki daftarin yarjejeniyar filla-filla a cikin makonni huɗu, domin ya yi bayanin matakin da za a ɗauka a gaba.

Wannan matsaya ta Majalisar Tarayya dai ta zo ne biyo bayan wani ƙorafin da mafi yawan ‘yan Najeriya ke ci gaba da yi na rashin amincewar su kan yadda ake zargin yarjejeniyar ta bada izni, dama da ‘yanci ga ‘yan maɗigo, masu luwaɗi, mata-maza da masu sauya halittar jikin su.

Shugaban Marasa Rinjaye, Aliyu Madaki daga Jihar Kano ne da wasu mambobin tarayya su 87 suka nemi a dakatar da aiki da yarjejeniyar.

Yarjejeniyar Samoa dai wata yarjejeniya ce tsakanin Ƙungiyar Tarayyar Turai da wasu ƙasashe 79, cikin su har da ƙasashen Afrika 48, ƙasashen Caribbean 16, na Pacific 15.

CIkin makon jiya ne jaridar Daily Trust ta buga labarin cewa za a bai wa Najeriya tukuicin lamunin Dala biliyan 150 saboda ta sa hannun amincewa da Yarjejeniyar Samoa, wadda ta halasta maɗigo, luwaɗi da maɗigo. Tuni dai gwamnatin tarayya ta ƙaryata, kuma ta yi barazanar maka jaridar kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button