Barazanar da NATO ke fuskanta a daidai lokacin da ta cika shekaru 75
Shugaban Amurka Joe Biden ya fara karɓar baƙuncin takwarorinsa shugabannin ƙasashe manbobin Ƙungiyar Tsaro ta NATO, wadda ta cika shekaru 75 da kafuwa, a daidai lokacin da ƙungiyar ke ƙoƙarin daƙile barazanar yaƙin da Rasha ke yi a Ukraine, da kuma ƙarfin ikon da China ke gwadawa a yankin Asiya da Pasifik.
Wani ƙarin ƙalubalen da shugabannin ƙasashen na NATO ke fuskanta yayin gudanar da wannan muhimmin taro shi ne rashin tabbas ɗin da ƙungiyar tsaron tasu ke fuskanta dangane da ɗorewarta.
Duk da cewar yaƙin da Rasha ta ƙaddamar kan Ukraine shekaru biyu da suka gabata ya zaburar da ƙungiyar, wadda aka kafa bayan yaƙin duniya na biyu domin kare nahiyar Turai daga barazanar Tarayyar Soviet, a halin yanzu haɗin gwiwar manbobin na NATO na fuskantar barazana, saboda wasu dalilai da suka haɗa da ƙarfin magoya bayan da masu zafin kishin ƙasa ke samu a ƙasashen Jamus da Faransa, waɗanda ka iya juya wa NATOn baya.
Sai kuma fargabar da ake ciki kan yiwuwar sake komawar Donald Trump kan shugabancin Amurka, wanda a wa’adin shugabancinsa na farko ya yi barazanar janye Amurkar daga kungiyar ta NATO, lamarin da ya tayar da hankalin manbobinta.
Masana da ke bibiyar lamurran da ke wakana sun ce babban abin da shugabannin NATO za su mayar da hankali a kai yayin taron da za su shafe kwanaki uku suna yi daga wannan Talata, shi ne ƙarfafa haɗin gwiwa tsakaninsu, da kuma jaddada dorewar tallafinsu ga Ukraine, duk domin tabbatar da tsaron nahiyar Turai.