Labaran Duniya

An Iso Da Gawar Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Wanda Ya Rasu Fiye da Shekaru Biyu da Suka Wuce A Landan

Kimanin shekaru biyu da watanni tara bayan rasuwarsa, gawar tsohon shugaban majalisar dattawa, Joseph Wayas, ta isa Najeriya Mista Wayas dai ya rike mukamin shugaban majalisar dattawa daga Oktobar 1979 zuwa Disambar 1983, kuma ya rasu ne a birnin Landan A lokacin wallafa wannan rahoto, an dauki gawar marigayin daga filin jirgi zuwa babban asibitin kasa da ke Abuja, domin shirin binne shi.

Mista Wayas, ya kasance shugaban majalisar dattawa tsakanin 1 ga Oktobar 1979 zuwa 31 ga Disambar 1983, kuma ya rasu yana da shekara 80 bayan ya yi fama da rashin lafiya.

An dai ruwaito cewa an doro gawar Joseph Wayas ne kan jirgin British Airways 083 daga Landan, kuma ya ta iso Abuja misalin karfe $:40 na Asubah.

An ce ita ma matarsa ​​ta rasu bayan kwanaki 12 da mutuwarsa amma an binne ta, sai ita gawar dan siyasar ce aka ajiye a dakin ajiye gawa na Landan, lamarin da ya jawo cece kuce.

Jarigbe Agom, Peter Akpanke, ‘yan uwa da sauran masu ruwa da tsaki daga ahalin Joseph Wayas ne suka tarbi gawar ta tare da ajiye ta a dakin ajiye gawa na babban asibitin kasa dake Abuja. Manyan baki sun fara zuwa ta’aziyya Da yake zantawa da manema labarai, Sanata Jarigbe ya gode wa gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu bisa yadda ya taimaka wajen dawo da gawar Joseph Wayas daga Landan.

Sanata Jarigbe Agom, mai wakiltar Cross River ta Arewa ya ce yana da yakinin cewa Gwamna Otu zai shirya gagarumin bikin binne tsohon shugaban majalisar, in ji rahoton Vanguard. Tun bayan isowar gawar ne aka ruwaito cewa manyan baki na ci gaba da sanya hannu kan littafin ta’aziyyar marigayin a gidan sa na Asokoro da ke Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button