Labaran Duniya
Wani Dan sumogal Ya Kade Jami’in Kwastam Da Mota Ya Mutu Har Lahira
Hukumar kwastam ta ce an kashe wani jami’inta mai mukamin Sufeto a ranar Juma’a a garin Achilafia da ke hanyar Daura zuwa Kano a jihar Jigawa.
Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da wani direban wata mota da ake zargin mai fasa kwauri ne da ke shigo da kaya ta barauniyar hanya ya bugi jami’in a lokacin da yake kokarin gujewa kama shi.
Inda nan take aka garzaya da ma’aikacin kwastam din zuwa babban asibitin Kazaure, daga bisani aka dauke shi zuwa cibiyar kula da lafiya ta tarayya (FMC) da ke Katsina inda likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarsa.