Shugaba Tinubu Ya Nada Sabuwar Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da naɗin Misis Didi Esther Walson-Jack, OON, a matsayin sabuwar shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, daga ranar 14 ga Agusta, 2024.
Wata sanarwar da ta fito daga ofishin mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ta bayana cewa Misis Walson-Jack za ta karɓi aiki ne daga Dr. Folasade Yemi-Esan, CFR wadda za ta yi ritaya a ranar 13, ga watan Augustan wannan shekarar.
An naɗa Misis Walson-Jack a matsayin Babbar Sakatariya ta Tarayya a 2017 kuma ta yi aiki a ma’aikatu da dama.
Sanarwar ta ƙara da cewa, yayin da Shugaba Tinubu ke miƙa godiyarsa ga shugabar ma’aikata mai barin gado, ya yi kira ga shugabar ma’aikata mai jiran gado da ta gudanar da aikinta cikin gaskiya da aminci kuma ta tabbatar da bin tsare-tsare da dokokin aikin gwamnati.