Labaran Duniya

Gwamnatin Jihar Zamfara Zata Bude Makarantun Kwana Da Suka Dade Da Rufewa 

 An kammala dukkan shirye-shiryen sake komawa makarantun Sakandaren Kimiyya ta  Gusau sakamakon kammala  ayyukan gina dakunan  kwanan dalibai da wurin karatunsu. 

 Kwamishinan ilimin kimiyya da fasaha na jihar Malan Wadatau madawaki ne ya bayyana haka ga manema labarai a yau, jim kadan bayan kammala duba dakunan kwanan dalibai da aka kammala.

 Ya ce, Gwamna Dauda Lawal tun daga hawan sa ya ayyana dokar ta-baci kan ilimi duba da yadda gwamnatocin baya a jihar suka yi watsi da harkan ilimi a jihar, a cewarsa, za a bude dukkan makarantun kwana da aka dade da rufewa sannu a hankali, musamman makarantun da babu barazanar tsaro.

  Madawaki ya kuma ce gwamnati ta samar da dukkan kayayyakin da ake bukata ga makarantar kimiyya ta Gusau, don haka a zangon farko na wannan shekara dukkan daliban za su koma kwana.

 Kwamishinan ya kuma kai irin wannan ziyarar zuwa kwalejin fasaha da kimiyya ta ZACAS ta Zamfara, inda ya duba masallaci da wurin kwanan daliban na mata, inda ya tabbatar da cewa kashi na biyu na aikin zai hada da gina  ajijuwa, da dakin kwanan dalibai maza, inda ya kara da cewa kashi na uku zai kunshi, gyaran gidajen ma’aikata da katange makarantar da gyaran ofisoshin malamai da hanyoyin sadarwa a cikin kwalejin.

 Da yake jawabi ga daliban, Malan Wadatau madawaki ya sanar da su da su zama jakadu nagari tare da yi wa gwamnatin Dauda Lawal Dare addu’a ta ci gaba da gudanar da ayyukan alheri da ta sa a gaba ,ya ce gwamnati ta shirya tsaf domin yin garambawul ga harkokin ilimi tun daga tushe har zuwa makarantun taraiya dake fadin jihar.

 Ya ce “Wannan don amfanin ku da ci gaban ku ne, ina kira gare ku da ku sadaukar da kanku kan karatunku, da neman ilimi, domin ta haka ne kawai jama’a za ku ci gaba a rayuwa, “Babu wata al’umma da ta ci gaba ba tare da ingantaccen ilimi ba, duk kasashen da suka ci gaba sun ci gaba ne saboda suna da ingantaccen tsarin ilimi.

 “Saboda haka a namu bangaren za mu samar da yanayi mai kyau da zai tabbatar da cewa dalibai da malamansu sun samu kwanciyar hankali ta yadda dalibai za su iya koyo, kamar yadda muka sani ba za a iya gudanar da koyo da koyarwa ba sai a yanayin da ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button