Labaran Duniya

Shugaba Tinubu Ya Sanar Da Sabon Albashi Mafi Kankanta Ga Ma’aikatan Najeriya

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da naira 70,000 a matsayin sabon albashi mafi ƙanƙanta ga ma’aikatan gwamnatin ƙasar.

Tinubu Ya Sanar Da Sabon Albashi ne a ganawarsa da wakilan ƙungiyoyin ƴan ƙwadago na ƙasar a ranar Alhamis.

Ministan yaɗa labaru na Najeriya, Mohammed Idris ya sanar da manema labaru cewa “ina farin cikin shaida muku cewa a yau (Alhamis) ƙungiyoyin ƴan ƙwadago na Najeriya da Gwamnatin Tarayya sun amince da wani ƙari a kan naira 62,000 a matsayin albashi mafi ƙanƙanta.

Sabon albashin mafi ƙanƙanta da ake sa ran shugaban ƙasa zai gabatar wa Majalisar Dokokin Tarayya shi ne naira 70,000.”

Wannan na zuwa ne bayan kwashe tsawon lokaci ana taƙaddama tsakanin ƴan ƙwadago da gwamnatin Najeriya game da sabon albashin mafi ƙanƙanta ga ma’aikata.

Ƙungiyar ƙwadago ta dage kan cewa wajibi ne gwamnatin ƙasar ta yi wa ma’aikata ƙarin albashi domin yin daidai da halin da ake ciki na rayuwa.

Tashin farashin kayan masarufi ya yi ƙamari a ƙasar mai yawan al’umma sama da miliyan 200.

Cire tallafin man fetur da shugaban ƙasar ya yi a ranar da ya karɓi mulki cikin watan Maris na shekara ta 2013, ya sanya farashin kayan masarufi ya nunnunka, lamarin da ya jefa al’ummar ƙasar cikin mummunan hali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button