TRUMP_ Zan yi korar baƙi da ba a taɓa yi ba a tarihin Amurka
Tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce idan ya sake zama shugaban kasar zai yi korar baki da ba a taba yi ba a tarihin kasar.
Trump ya fadi hakan ne yayin da yake gabatar da jawabin amincewa da takarar da jamiyyarsa ta Republican ta ba shi a zaben shugaban kasar da za a yi a watan Nuwamba, a wajen babban taron jam’iyyar da aka shiga rana ta hudu kuma ta karshe a Milwaukee.
Ya yi bayani kan yunkurin kashe shi da wani dan bindiga ya yi a ranar Asabar, inda ya bayyana irin halin da ya ce Amurka da duniya sun shiga bayan shugabancinsa tare kuma da irin matakan da zai dauka idan har ya sake dawo wa kan shugabancin a zaben da za a yi a watan Nuwamba.
Donald Trump wanda ya shafe sama da sa’a daya yana gabatar da jawabin nasa wanda galibi kusan da ka yai maimakon a ce jawabi ne a rubuce, ya fara ne da kiran neman hadin kai.
Shugaban ya ce yanzu lokaci ne na sauyi, kafin kuma daga bisani ya shiga gabatar da alkawura daban-daban ga Amurkawa.
A jawabin ya bayyana yadda ya tsallake rijiya da baya a yunkurin da wani dan bindiga ya yi na hallaka , inda ya ce, hankalinsa bai tashi ba, domin Allah yana tare da shi a.
Ya bayyana yadda ya ji lokacin da harsashin ya same shi a kunne;
”lokacin da na ji kara na ji wani abu ya buge ni, da karfi sosai a kunnena na dama. Sai na ce wa kaina, Kai mene ne wannan? Kai wannan harsashi ne kawai, na kai hannuna na dama wajen kunnena, na sauko da hannuna , hannuna duk jini.’’
Tsohon shugaban ya yi alkawarin rage hauhawar farashin kayayyaki da kawo karshen shiga kasar da bakin haure kanyi, inda ya yi alkawarin kammala ganuwar da ya fara wadda za ta raba Amurka da Mexico, inda bakin haure kan bi su shiga.
Ya ce zai kawo karshen shigar bakin haure nan take a ranar farko inda zai rufe iyakar.
A kan halin da duniya take ciki na rikici kuwa ya yi alkawarin dakatar da yake-yake , wadanda ya ce da shi ne a kan shugabancin Amurka da ma ba a fara su ba.
Ya ce duniya na dab da fadawa yakin duniya na uku, ya yi alkawarin dakatar da yakin Ukraine da Gaza.
Haka kuma ya soki Shugaba Biden da cewa ya yi illar da ta fi wadda gurbatattun shugabannin Amurka goma suka yi jumulla a tarihi.
Donald Trump ya soki abokin hamayyarsa tasa kan haifar da matsalar hauhawar farashi, da shigar bakin haure da sauran matsaloli da rikce-rikice na duniya.
Ya yin da yake wannan shi kuwa Shugaba Biden wanda ke can killace a gida a Delaware yana neman murmurewa daga cutar Korona, bayan dakatar da yakin neman zabensa kwatsam, yana kara shan matsin lamba daga jiga-jigan jam’iyyarsa ta Democrat kan ya hakura da takarar zaben na na watan Nuwamba.
Daga cikin masu neman shawo kansa ya hakura da takarar an ce yanzu akwai tsohuwar shugabar majalisar wakilai ta Amurka Nancy Pelosi, wadda ta nuna masa sakamakon wasu alkaluma na yadda zaben zai iya kasancewa.
Hak shi ma tsohon mai gidansa, kuma tsohon shugaban Amurkar, Barack Hussein Obama, ya nuna shakku kan yadda Biden zai yi nasara a zaben.
Shugaba Biden din dai ya kafe akan sai ya yi takarar, kodayake wasu bayanai na nuna cewa akwai alamun kila ya hakura.