Akalla Ƴan Boko Haram 263 Ne Suka Miƙa Wuya – Rundunar MNJTF
Rundunar Sojojin Haɗin Gwiwwa mai Yaƙi da Boko Haram a Tafkin Chadi ta ce mayaƙan ƙungiyar tare da iyalansu kusan 263 ne suka miƙa wuya ga sojojinta da ke aiki a yankin tafkin Chadi.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce ‘yan ƙungiyar sun fara rububin miƙa wuyar ne daga ranar 11 ga wtan Yulin, lokacin da wasu mutum biyar suka miƙa wuya ga sojoji a garin Wulgo da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru.
A ranar ne kuma, wasu ‘yan ƙungiyar 19 suka miƙa wuya a wani ƙauye da ke yankin Arewa Mai Nisa a Jamhuriyar Kamaru.
Cikin waɗanda suka miƙa wuyar akwai mata da ƙananan yara da kuma matasa, kamar yadda sanarwar ta yi bayani.
Sojojin sun ce a ranar 15 ga watan na Yuli wasu ƙarin mutum 102, da suka haɗa da matasa 20 da mata 40 da ƙananan yara 42 ne suka miƙa wuya da yankin arewa mai nisan.
Binciken farko ya gano cewa waɗanda suka miƙa wuyan ‘yan Najeriya da Kamaru ne, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske, tana mai cewa an miƙa ‘yan Najeriyar daga cikinsu hannun sojojin rundunar Operation HADIN KAI, domin ɗaukar mataki na gaba.