Uncategorized

Sanata Marafa Ya Naɗa Kwamitin Jagorancin Jam’iyyar APC Na Bangarensa

A ranar Asabar din data gabata ne Sanata Kabiru Garba Mafara ya kafa kwamitin mutum 21 na jam’iyyar APC mai kula da ɓangarensa a jihar Zamfara.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron sirri da mambobin kwamitin, shugaban kwamitin, Hon. Surajo Maikatako ya bayyana cewa rashin adalci da kyakkyawan shugabancin jam’iyyar da shugaban Jam’iyar ke yi a jihar ne ya jawo rabuwar ɓangaren Sanata Kabiru Garba Marafa.

A cewarsa, kwamitin zai bai wa haɗin kai da cigaban jam’iyyar muhimmanci a jihar, yana mai jaddada cewa kwamitin zai yi bakin ƙoƙarinsa wajen ganin an yi wa ɗaukacin magoya bayan jam’iyyar da Sanata Kabiru Marafa adalci.

“Rashin adalci da rashin kyakkyawan shugabancin jam’iyyar APC a jihar ya kai ga kafa kwamitinmu da Sanata Kabiru Marafa ya yi, kuma ba za mu cigaba da sa ido a kan shugabancin jam’iyyar dake neman tarwatsewa da kawo cikas ga zaman lafiya, cigaba da haɗin kan jam’iyyarmu da mambobinmu a jihar ba”, inji Maikatako.

Maikatako ya ci gaba da cewa, kwamitin da ke ƙarƙashinsa zai cigaba da jajircewa wajen ganin jam’iyyar ta samu cigaba, yana mai kira ga magoya bayan Marafa da su kasance masu bin doka da oda domin cigaban jam’iyyar a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button