Gwamnoni Da Ministoci Zasu Yi Taro Yau Domin Haɗa Kai Su Dakatar Da Zanga-zanga
Gwamnatoci da ministoci za su yi taro yau domin haɗa kai su dakatar da zanga-zangar yunwa da ake shirin yi a fadin Najeriya
Gwamnatin tarayya ta ce a shirye ta ke ta tattauna da shugabannin zanga-zangar da aka shirya yi a fadin kasar da za a yi a ranakun 1-10 ga watan Agusta.
A wani taron gaggawa da aka yi a Abuja ranar Laraba, an kuma umurci dukkan ministocin gwamnatin tarayya da su ziyarci jihohinsu daga ranar Laraba 24 ga watan Yuli zuwa ranar Alhamis 1 ga watan Agusta, lokacin da aka shirya fara zanga-zangar. Su yi wa jama’a bayanin irin cigaban da suka samar a tsawon hawan su sannan su rarrashi jama’arsu kada su fita zanga-zangar,
Majiyar A Yau ta ruwaito sannan an zaɓi wasu ministoci da za su gana da gwamnonin jihohi a taron majalisar tattalin arzikin kasa da za a yi yau Alhamis a zauren majalisar da ke fadar Aso Rock Villa, domin haɗa kai da Gwamnonin wajen ganin su ma sun yi bakin ƙoƙarinsu wajen dakatar da zanga-zangar
Waɗannan kadan kenan daga cikin shawarwarin da aka yanke dauka a wajen taron gaggawa da aka yi tsakanin sakataren gwamnatin tarayya, George Akume da dukkan ministoci a Abuja da safiyar jiya Laraba.